Addini

Bishop Kukah, Sultan sun yi Allah-wadai da kisan ɗalibar da ta yi ɓatanci ga Annabi [S.A.W]

Arewa Times Hausa a baya ta habarto cewa wasu dalibai maza a Shehu Shagari College of Education Sokoto sun kashe wata ɗaliba har lahira bisa ɓatanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Haka zalika, Arewa Times Hausa ta sake bada labarin cewa kisan ɗalibar wacce aka bayyana sunan ta Deborah Samuel ya janyo martani daga ɓangarori daban-daban a faɗin Najeriya.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun sakataren Majalisar Sarkin Musulmi Sa’idu Muhammadu Maccido, yayi Allah wadai da kisan baki daya.

Advertisement

“Sultanate Council tana takaici abubuwan da suka faru a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, wadanda suka yi sanadin rasa rayuwar wata dalibar makarantar.

Sanarwar ta kara da cewa “Majalisar Sarkin Musulmi ta yi Allah-wadai da lamarin baki daya, sannan ta bukaci jami’an tsaro da su gurfanar da wadanda suka aikata wannan lamari na rashin hankali a gaban kuliya.”

A nasa bangaren, Bishop na cocin Katolika na Sokoto, Bishop Mathew Kukah, yayin da ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika, ya kuma yi kira ga hukumomi da su gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da duk wadanda suka aikata laifin.

A cewar wata sanarwa da Bishop Kukah ya sanya wa hannu, kuma ya bayyana wa wakilin mu, “abin da ya rataya a wuyan dangin ta, hukumar makarantar shi ne tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan ta’asa ta rashin ƙaunar dan-adam, ko da kuwa ta dalilin su ne, ana ladabtar da su bisa ga dokokin ƙasar mu.

“Wannan bai da alaƙa da addini. Kiristoci sun zauna lafiya da makwabta musulmi a nan Sokoto tsawon shekaru.

“Dole ne a dauki wannan lamarin a matsayin wani laifi babba, kuma dole ne doka ta dauki mataki.”

Sai dai Kukah yayi kira ga Kiristocin Sakkwato da kewaye da su kwantar da hankalin su tare da yiwa marigayin addu’ar Allah ya jikan ta.

Advertisement