Al'umma

Birai sun ƙwace kayan gwajin COVID-19 daga marasa lafiya

INDIYA – An ba da rahoton cewa wasu birai sun kai hari kan dakin gwaje-gwaje kuma sun tsere da tarin mayan cutar coronavirus.

A cewar jaridar Times of India, wani abin al’ajabin da ya faru ne lokacin da birqn suka kai harin a kusa da Kwalejin Kiwon Lafiya ta Meerut da ke birnin Delhi na Indiya.

Daga nan dabbobin suka kwace samfuran gwajin COVID-19 daga majiyyata uku suka gudu.

Advertisement

Daga baya an ga daya daga cikin birai a bisa bishiya yana tauna daya daga cikin kayan tattara samfurin COVID-19, jaridar Times of India ta ruwaito – ta kara da cewa dole ne a sake daukar samfurin gwaji daga marasa lafiya.

Advertisement