Labarai
Binance Zai Katse Duk Harkokin Naira (NGN) Ta Najeriya
Sakon email din Binance zuwa duk yan Najeriya masu amfani kamfanin!
Mun lura cewa a halin yanzu kuna da NGN a cikin asusun ku. Muna so mu sanar da ku cewa ba za mu ƙara bada sabis a cikin Nairar Najeriya (NGN) ba, wanda ke nufin ba zaku iya yin ciniki ta hanyar NGN ba.
Haka zalika, muna bada shawarar cewa masu amfani su cire NGN ɗin su, su yi musayar kadarorin su na NGN, ko su canza NGN zuwa cryptocurrency kafin mu daina ba da sabis na NGN.
Sannan kuma sauran balance na NGN a cikin Spot na masu amfani zamu sauya kuɗin zuwa USDT a madadin masu amfanin da kamfanin, ta yin amfani da ƙimar canjin 1 USDT = 1,515.13 NGN.
Wannan sakon Binance ya tura yan Najeriya shi ne a ranar Alhamis 7/3/2024, da safe 5:04.