Addini

Bidiyon Yadda Wani Bahaushe a Kano Ya Gudanar da Aikin Hajji a Filin Jirgin Sama Bayan Baisamu Zuwa Makkah Ba

Kanawa masu abin mamaki kalli yadda wani mutum ya gudanar da aikin hajjin sa a filin jirgin sama.

Wani dattajo a garin Kano ya gudanar da aikin hajjinsa a filin jirgin sama sakamakon tafi da jirgi yayi babu shi.

Mutumin dai ya koka da rashin tsarin gwamnati da kuma hukumar jigilar alhazai ta Kano ganin nuna rashin kulawa gamaniyata.

Mutumin dai ya nuna rashin jin dadin sa akan faruwar hakan domin har gatse yayiwa gobnan Kano Abdullahi Umar ganduje inda yace abinda yayi mana Allah yayi masa.

Dattijon da akalla zai kai shekara 60 ya magantu cikin bachin rai daganin yadda jirgin ya tashi ya tafi ya barshi.

Idan baku manta ba wannan shekarar dai mahajjata na Kano sun fuskanci kalu bale da yawa inda har takai wasu sun karbi kudin su sunyi fushi sunce sai wata shekarar.

Kome ke jawo faruwar hakan?
Allah dai ya kiyaye faruwar haka a shekara ta gaba.

Back to top button