Al'umma

Bidiyo: Wani Matashi Ɗan “Yahoo” Ya Haukace A Cikin Layi Bakin “ATM”

Wani yaro dan yahoo ya haukace a kwanan nan yana jiran layin zai ciro kudi daga bakin na’urar cirar kudi ta ATM.

Kamar yanda wani faifan bidiyo da aka wallafa a yanar gizo, matashin na tsaye a kan layi a wani reshen bankin Stanbic da ke jihar Legas, sai aka ga ya fara alamun na mahaukata.

Ba tare da ya tanka ba, ya sunkuyar da kansa yana kallon kasa na tsawon mintuna da dama yana jiran a layi – ya jawo hankalin wasu kan layin.

Da sauri muat8 suka nufi kudu lokacin da ya jefar da jakar sa dake rataye a wuyan shi, kuma ya cire rigar ijikin shi ya fara ihu.

An ji mutumin na da ake zaton fan Yahoo yana ihu yana cewa “Zan kashe mahaifina” a cikin faifan bidiyon, yayin da yake bin wani da ke wurin.

Kalli lamarin a cikin bidiyon da ke kasa.

Advertisement