Tsaro

Bidiyo: Jawabin Wani Ɗan Ta’adda Dake Da Alaƙa Da Bafarawa Da Bello Turji

Idan dai ba’a manta a kwanakin baya ne wasu yan ta’adda karkashin jagorancin wasu na hannun damar Bello Turji Kachalla suka hallaka wasu jami’an tsaro a karamar hukumar mulki ta Sabon Birni, Isa a Jihar Sakkwato.

Jami’an tsaron da aka kashe a lokacin sun haɗa da, sojoji, ƴan sanda da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (Civil Defence).

Bayan wannan mummunan harin, jami’an yan sanda sun yi aiki tukuru domin bankaɗo masu a hannu a wannan aika-aikar.

Advertisement

Cikin ikon Allah jami’an tsaron sun samu nasarar cafke wani mashahurin dan ta’adda wanda ke da alaƙa da tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa, sannan kuma a bangar ɗaya kuma shi babban na hannun damar Bello Turji ne.

Bayan cafke shi, ya yiwa jami’an tsaro bayani dalla-dalla game da ayyukan su da kuma alaƙar shi da da Bafarawa da kuma Turji.

Domin kallo da sauraron abin da wannan dan ta’addan ke ya bayyana, sai ku kalli wannan bidiyo dake a ƙasa;

Advertisement