Siyasa

BIDIYO: Ina Shakkun Goyon Bayan Buhari Ga Takarar Tinubu – Yakasai

Wani dattijon kasa, Alhaji Tanko Yakasai ya ce yana da shakku kan goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Tanko Yakasai, wanda ya bayyana goyon bayan sa ga Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ake hira da shi a gidan talabijin na Control TV.

Ya ce, “Abin da na gane shi ne, ban da tabbacin ko Buhari ya ji dadi da takarar Tinubu, wannan shi ne batun, shi APC ne saboda shi ne shugaban da aka zaba a dandalin APC amma ya shin Buhari ya jajirce kan na Tinubu? Ina da shakka.”

Advertisement

Da aka tambaye shi ko yana ganin Buhari yana goyon bayan dan takarar PDP?

Ya ce, “Ban sani ba amma ban ga jajircewar shi ba na goyon bayan takarar Tinubu a APC ba. Ban tabbata ko APC ce ko a’a ba amma tabbas, halayen Tinubu ba zai faranta masa rai ba daga kimanta halin da nake ciki.”

Advertisement