Taskar Labarai
Trending

Bidiyo: Dan Tiktok Yahaya Shareef Ya Tabbatar Da Yana Cikin Yan Luwadin da Aka Kama Amma Zaiyi Karin Bayani

Wani fitaccen dan TikTok da Instagram, Yahaya Shareef ya bayyana cewa shi ne a cikin wani bidiyo wanda ake ta yadawa wanda ‘yan sanda su ka titsiye ‘yan luwadi a Jihar Kano.

Matashin wanda ya samu shahara a kafafen sada zumuntar zamani ya dade yana daukar hankalin jama’a tun daga kyawun siffarsa da kuma iya sanya suttura.

➡️Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Jarumi Kabiru Na Kwango Ayau Daga Bakin Abba Elmustapha

Har ila yau, ana ganin hotuna da bidiyonsa a Dubai, Saudi Arabia da sauran kasashe, wani lokacin ma har tare da ‘yan uwansa da mahaifiyarsa.

Ana ganinsa yana rike da tsadaddun wayoyi a cikin falo da dakuna na alfarma inda yake hawa kan wakoki tare da kwasar rawa.

Sai dai kwatsam sai ga wani bidiyo ya bayyana wanda ‘yan sanda su ka titsiye shi a matsayin daya daga cikin wadanda ake zarginsu da aikata luwadi da damfara.

➡️Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Jarumi Kabiru Na Kwango Ayau Daga Bakin Abba Elmustapha

Ganin bidiyon ya fara bazuwa ne yayin da wasu ke cewa shi ne wasu kuma su na musantawa yasa ya fito fili ya bayyana gaskyar abinda ya sani.

A cewarsa, tabbas shi ne a cikin bidiyon amma idan jama’a sun kula dakyau bai amsa laifin yin luwadi ko kuma damfarar kowa ba.

Ya ce ko a lokacin ‘yan sanda ne su ka tasa shi gaba inda su ka tilasta masa amsa laifin da bai aikata ba. Amma kuma lokaci ya yi da zai yi bayani dalla-dalla.

A cewarsa, shekaru 4 kenan da faruwar lamarin kuma wasu ne su ka shirya hakan musamman don tozarta shi, amma a lokacin da yayi bidiyon yana wani aiki ne, daga baya zai natsu ya fallasa sunaye.

➡️Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Jarumi Kabiru Na Kwango Ayau Daga Bakin Abba Elmustapha

Ya ce Allah ya rufa masa asiri don kasuwancinsa yake yi. Idan akwai wanda ya san ya neme shi, ya fito ya bayyana wa duniya.

Kuci gaba da kasancewa da ArewaTimes domin Jin yadda zata kasance, dakuma labaran yau da kullum na ciki da wajen Nigeria.

➡️Gaskiyar Magana Akan Mutuwar Jarumi Kabiru Na Kwango Ayau Daga Bakin Abba Elmustapha

Back to top button