Bello Turji Ya Sanar Da Ƙwace Manyan Motocin Yaƙi Biyu Na Sojojin Najeriya Bayan Wata Gwabzawa
Hotunan bidiyo sun bayyana a yanar gizo na Sarkin ‘yan fashi, Bello Turji da ’yan kungiyarsa suna murnar karbe manyan motocin yaƙi biyu na Sojojin Najeriya.
Turji da ‘yan kungiyarsa sun kuma karbe harsashi da dama daga hannun sojojin Najeriya a lokacin da suka kama motocin.
Wani kwararre kan harkokin tsaro da yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ZagaZola Makama ya tabbatar da hakan.
Makama ya ce an samu rahoton tashin hankali daga rundunar da ke nuni da wani babban taron ‘yan bindiga a wani wurin da aka kebe a sansanin Bello Turji.
Da yake mayar da martani, an tura tawagar sojoji cikin gaggawa zuwa yankin, wanda wani matashin jami’i ya jagoranta amma motar tawagar ta makale a cikin wani wuri mai dausayi, wanda ya hana su ci gaba.
Makama ya bayyana cewa, sojojin sun fuskanci munanan harbe-harbe daga ‘yan bindigar, lamarin da ya haifar da mummunar harbe-harbe da aka kwashe na wasu sa’o’i.
“Saboda yanayin (yawan ruwan sama), a tsawon yini, tallafin sama ya kasa iso da sauri, wanda hakan ya baiwa ‘yan fashin damar karfafa matsayinsu.
“Sojojin sun yi yunkurin yin amfani da dayan motar MRAP wajen ciro daya amma ta makale a cikin laka ita ma.
“Wasu tawagar dakaru aka aika su zuwa wurin amma kafin isowarsu, lamarin ya mamaye wadanda ke rike da filin domin sun kasa fitar da MRAPS guda biyu.
“Sojojin sun janye, sun bar motocin. Ba a sami rahoton mace-mace a gwabazawat ba.
“Sa’o’i kadan bayan haka, Turji da yaransa sun bayyana a wurin suna harbi a sama suna kururuwa cewa sun kori sojojin tare da daukar motocinsu.”
Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.