Tsaro

Bello Turji Ya Riƙe Mutane 5 Bisa Rashin Cika Kuɗin Fansar Garin Su Miliyan ₦20, Har Sai An Cika Su

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, yayi garkuwa da wasu mazauna unguwar Moriki da ke jihar Zamfara, bisa rashin cika ‘kudin zaman lafiya.

Bello ya dorawa al’ummar harajin Naira miliyan ₦20,000,000 wanda daga cikin su suka iya biyan Naira miliyan 10.500,000.

An tattaro cewa fitaccen shugaban ‘yan fashin da ya addabi al’umomi da dama a jihar Zamfara ya kame ‘yan kabilar Moriki da suka kawo kudin zaman lafiya har sai an kammala biyan sauran.

Idan ba’a manta ba kwanan ba mu bada rahoton cewa wata al’umma na shirin haɗawa dan ta’addan miliyan ₦20,000,000 na zama lafiya.

Advertisement