Tsaro

Bello Turji Na Ciki Ɓacin Rai Ne Saboda An Kai Mai Miliyan ₦10.6 Daga Cikin Miliyan ₦20 Na Fansar Gari – Sani

Karin bayani kan yadda wasu mazauna jihar Zamfara ke tashi-fadi don tsira da rayukan su game da makudan kudaden harajin Naira miliyan ₦20 da ɗan ta’addan nan mai suna Turji ya dora musu. A wasu bayanai na na baya-bayan nan da mazauna garin Moriki da ke da tazarar kilomita 33 a kan titin Kaura Namoda zuwa Shinkafi, da Turji ya sanya wa al’umma harajin Naira miliyan ₦20.

A cewar rahoton, mazauna yankin sun iya tara Naira miliyan ₦10.6 daga cikin Naira miliyan ₦20 amma Turji ya fusata da karancin kudi, inda ya yanke shawarar cafke mutum biyar daga cikin mutane bakwai da suka zo ba shi kudin.

A cewar wani mazaunin unguwar Sani Moriki, bayan da Turji ya dora masu wannan harajin tare da neman su biya su kudin nan da makonni 2, al’ummar yankin sun yanke shawarar cewa kowane iyali zai biya Naira ₦6,500. Sai dai wasu iyalai sun kasa biya don haka sun samu damar tara Naira miliyan ₦10.6 kacal.

Advertisement

Sani Moriki ya bayyana cewa mutane bakwai daga cikin al’ummar yankin ne suka kai kudin zuwa ga Turji da ke kusa da Kasayawa, al’ummar da ke da tazarar kilomita 1 daga gabashin garin Moriki. Da Turji ya ga kudin Naira miliyan ₦10.6 ne kawai, sai ya fusata ya yanke shawarar yin garkuwa da biyar daga cikin mutanen bakwai. Sani Moriki ya bayyana cewa sun tuntubi Turji tare da yi masa alkawarin za su kawo ragowar Naira miliyan ₦9.4, cikon miliyan ₦20 da ya bukata.

Advertisement