Kasuwanci

Bayanai sun nuna cewa China na sayen man Iran fiye da yadda ta ke saye kafin takunkumi

Sayayyar man da China ta yi na man Iran ya karu a watannin baya-bayan nan, wanda ya zarce kololuwar na shekarar 2017 a lokacin da cinikayyar ba ta shafi takunkumin Amurka ba, kamar yadda bayanan binciken dakon kaya suka nuna.

Haɓaka sayayyar da babbar mai shigo da man fetur na duniya ya yi yazo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa tsakanin Teheran da manyan ƙasashen duniya don farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 wadda za ta ɗage takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ɗin. Tattaunawar ta kara tsananta a yan makonnin nan.

Maido da man fetur na Iran zai saukaka matattarar kayayyaki a duniya da sanyin farashin danyen man da ya kai dala $100 kan ganga daya biyo bayan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

Advertisement
Advertisement