Siyasa

Bayan Zaɓen Fidda Gwani, Atiku Ya Ce Min Yana So A Cire Ayu Daga Ofis – Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yana magana ne a wata hira da ya yi da BBC a kwanakin baya inda ya bayyana cewa Atiku ya zo wurin shi ya shaida mai cewa a tsige Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

A cewar Wike, Atiku ya zo ganin shi ne bayan kammala zaben fidda gwani a gidan shi da ke Abuja inda ya bukaci a tattauna da shi. A tattaunawar ta su Atiku ya ba da shawarar a tsige Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP. Da ya tambayi dalilin hakan, Atiku ya shaida mai cewa zaman Ayu a matsayin shugaban PDP ya sabawa al’adar shiyya ta jam’iyyar su.

Ya kuma bayyana cewa bai ji dadi ba saboda Atiku bai zo mai ba bayan ya sauya ra’ayin shi game da tsige Ayu a matsayin shugaban PDP na kasa.

Advertisement

Yace;

“Mun je ofishi na a gida na da ke Abuja, ka san fushi na ko daya daga cikin abubuwan da suka sa ni fushi, na tattauna da kai (Atiku), na girmama ka, ka fada min wani abu, wanda ban sani ba, ashe ba da gaske kake game da shi ba, babu wani laifi a cikin shugabanci da za a ce duba, ba na jin wannan zai iya aiki a yanzu, na fi son shi.

Ko da mafi munin abin shi ne, da son ranka ya fito daga gare ka, don lokacin da muka zauna, sai (Atiku) ya ce, ka duba sai ya zo ya ganni, na ce lafiya ba matsala, ya ce to primaries sun zo sun tafi. Na ce ba matsala na san ka yi tunanin zan je kotu, a’a ba zan je kotu ba, bana son jam’iyyar mu ta mutu.

Yace toh, yana ganin dole Ayu ya tafi, nace me yasa, yace saboda ba al’ada bane shugaba da dan takarar shugaban kasa su fito daga shiyyar daya…

“Wannan ne kawai lokacin da Atiku ya zo gani na bayan zaben fidda gwani a ranar Litinin.”

Advertisement