Laifuku

Bayan Yan Mata 10 Sun Haihu, Maigida Na Ya Ba Ni 500,000, Ya Sayar Da Jariran

Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta cafke wani yaro dan shekara 17 mai suna Noble Uzuchi bisa zargin shi da yiwa wasu mata 10 ciki a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Grace Iringe-Koko ne ya gabatar da wanda ake zargin a ranar Juma’a tare da Chigozie Ogbonna, wani mutum mai shekaru 29. A cewar wanda ake zargin wanda ya amsa laifin shi, ya bayyana cewa yana aiki ne da wasu mutane biyu wadanda suka kasance manyan shi a kasuwancin kuma dukkan su sun mallaki masana’antar jarirai tare a jihar, inji rahoton Daily Post.

Ya bayyana sunayen manyan shi a matsayin Favour Bright and Peace Alikoi. Sai dai a yayin da wanda ake zargin, Noble Uzuchi ke zantawa da manema labarai, ya amsa da cewa, “Bayan matan 10 sun haihu, sai shugaba na ya biya ni Naira 500,000 ya sayar da su.

Advertisement

Yayin da ya ke ci gaba da magana, ya ce bayan an biya shi diyya da makudan kudade, sai maigidan na shi ya kwashe jariran daga hannun masu shayarwa ya sayar da su. Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya bayyana cewa an ceto mata masu juna biyu 10 bayan sun kai samame tare da cafke mutanen biyu.

Advertisement