Kasuwanci

Bankin Duniya ya dakatar da duk wasu ayyuka a Rasha da Belarus akan mamaye Ukraine

Bankin Duniya ya sanar a ranar Laraba cewa zai dakatar da duk wasu shirye-shirye a Rasha da Belarus saboda mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

Sanarwar da bankin ya fitar ta ce, “Bayan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine da kuma tashe-tashen hankula a kan mutanen Ukraine, kungiyar Bankin Duniya ta dakatar da dukkan shirye-shiryen ta a Rasha da Belarus ba tare da bata lokaci ba.”

Sanarwar ta kara da cewa Bankin Duniya bai amince da wani sabon lamuni ko saka hannun jari a Rasha ba tun daga shekarar 2014. “Haka zalika babu wani sabon lamuni da aka amince wa Belarus tun tsakiyar shekarar 2020.”

Advertisement
Advertisement