Kasuwanci

Ban Da Labari Mai Dadi Ga Mutanen Da Ke Kiran A Kara Lokacin Karbar Tsofaffin Kudi – Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ce bai da a wani labari mai dadi ga mutanen da ke ganin ya kamata a sauya wa’adin karbar tsoffin kudade.

Ya bayar da uzuri ne a yayin wani zama da ya yi da manema labarai, inda ya ce dole ne ya bayyana ra’ayin shi game da hukunce-hukuncen da suka shafi wa’adin kawar da tsofaffin kudaden Najeriya.

A cewar shi, dalilin da ya sa aka yanke wannan shawarar shi ne, kwanaki 90 sun fi isa ga masu tsohon kudade su yi kokarin saka su a bankuna. Ya bayyana cewa CBN ya dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da cewa dukkan bankunan Najeriya sun bude domin karbar duk tsoffin kudaden.

Advertisement

Godwin Emefiele ya bayyana cewa CBN ya yi kira ga bankunan Najeriya da su tsawaita sa’o’in aikin banki har ma a bude ranar Asabar a wani yunkuri na ganin an samu isasshen lokacin da mutane za su iya ajiye kudaden da suke hannun su. Ya bayyana cewa bankunan ba su bude ranar Asabar ba saboda ba su fuskanci irin gaggawar da suke tsammani ba. Kalli bidiyon anan.

Advertisement