Siyasa

Ban Baiwa Yan Najeriya Kunya Ba, Na Cika Alkawurra Na – Buhari

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a ranar Litinin, a jihar Bauchi, ya ce bai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba, sakamakon alkawuran da ya yi a yakin neman zabe a zabukan 2015 da 2019.

“Ban baiwa kowa kunya ba,” Buhari ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Adamu a lokacin da ya ziyarci Bauchi a ci gaba da taron yakin neman zaben shugaban kasa da na Gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress.

Da ya hangi taron jama’ar da suka tarbe shi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, Buhari ya yi ikirarin cewa hakan na nuni ne da nuna soyayya da aminci a gare shi daga ‘yan Najeriya.

Advertisement
Advertisement