Tsaro

Bam ya tashi a sansanin sojoji da ke babban jihar Taraba, Jalingo

Wata fashewa da ake kyautata zaton fashewar bam ce ta sake tashi a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

Fashewar wadda ta faru a ranar Talata da misalin karfe 9 na dare, ta afku ne a wasu yan mitoci daga sansanin sojoji dake cikin babban birnin Jalingo.

Wata majiya da ta zanta da DAILY POST, ta ce wani mai wucewa ne ya jefa bam din a cikin sansanin sojoji.

Fashewar, kamar yadda aka sani, na zuwa ne bayan wata guda bayan wani abu makamancin haka ya afku a yankin Iware da ke karamar hukumar Ardo-Kola wanda yayi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyi.

Back to top button