Al'umma

Babban Ciwon Kan Mu A Yaƙin Da Ake Yi Da Ƴan Ta’adda Sune Masu Leken Asiri – El-Rufai

Hoto: Maryam, matar aure da aka kama dake alaƙa da yan yan bindiga kuma take kai musu mata a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi ikirarin cewa babban abin da ke kawo cikas ga yaki da yan fashi da ta’addanci a jihar su ne masu ba da labari da ke fallasa bayanai ga masu laifi.

El-Rufai, wanda ya bayyana hakan a wajen bikin tunawa da ranar tunawa da sojojin kasar da aka gudanar a Kaduna, babban birnin jihar a ranar Asabar, yace “masu yada labarai ga yan ta’adda da ke zaune a cikin al’ummomin jihar na kawo cikas ga yakin da muke yi da yan fashi.

“Matsalar rashin tsaro da muke fuskanta a kasar nan, musamman a nan Jihar Kaduna, abin damuwa ne matuka, kuma ina ganin jami’an tsaro, musamman sojoji da yan sanda suna yin iya kokarinsu amma muna bukatar kowane mai ruwa da tsaki domin bayar da gudunmawa. Mun gano cewa babbar matsalar da muke da ita ita ce masu ba da labari ga yan ta’adda dake zaune a cikinmu.”

Advertisement

Gwamnan ya bukaci shugabannin addini da na al’umma a jihar su wayar da kan al’ummarsu da su kara daukar matakan tsaro da kuma kai rahoton duk wanda ya samu matsala ga hukumomin tsaro.

“Ina ganin yana da kyau shugabannin addini da na al’umma ba wai kawai su kara wayar da kan jama’a ba, har ma su lura da mutanen da ake ganin suna kashe makudan kudade ba tare da wata tabbatacciyar hanyar rayuwa ba, watakila masu satar mutane ne; su kai rahoto ga hukumomin da ke kusa da su.

“Muna ba da tabbacin cewa wannan gwamnati za ta kare irin wadannan bayanai kuma za ta dauki dukkan matakan da suka dace,” in ji shi.

Advertisement