Siyasa

“Ba zamu yi watsi da Burkina Faso ba saboda juyin mulki” – ECOWAS

Wakilin kungiyar kasashen yammacin Afirka ya ce zasu cigaba da yin aiki tare da Burkina Faso duk da damuwar da ake da shi kan shirin sojoji na rike madafun iko na tsawon shekaru uku bayan juyin mulkin da aka yi a watan Janairun 2022.

Kalaman sun fito ne a ranar Alhamis daga bakin ministar harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchway wadda ta jagoranci tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS zuwa Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso.

“Batutuwa da matsalolin da suka addabi Burkina Faso sune matsalolin mu, haka nan. Ba a wannan lokaci na bukatar Burkina Faso ba ne kungiyar ECOWAS za ta yi watsi da ita ba,” inji ta bayan ganawa da jagoran juyin mulkin kuma shugaban rikon kwarya Paul-Henri Damiba.

Ayorkor Botchway ya ce duk da haka hukumar ta damu da wa’adin shekaru uku na mika mulki ga mulkin dimokuradiyya amma shugabannin sojoji sun bayyana dalilansu.

Kungiyar ECOWAS dai ta dakatar da Burkina Faso ne bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Roch Kabore, sai dai ba ta sanya takunkumi kamar yadda ta yi wa makwabciyarta Mali da Guinea, inda kuma aka yi juyin mulki cikin watanni 18 da suka gabata.

Aika Da Wannan Labarin: