Kasuwanci

“Ba Gudu, Ba Ja Baya” Kan Wa’adin Daina Amfani Da Tsofaffin Kudi – Emefiele

Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, ya bayyana cewa babban bankin ba zai kara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan ne yayin taron MPC, wanda ya gudana ranar Talata a Abuja.

Emefiele ya ba da hakuri, yana mai cewa, “Ba ni da labari mai dadi ga wadanda suke ganin ya kamata mu sauya wa’adin.”

Advertisement

Ya yi ikirarin cewa ’yan Najeriya na da isasshen lokacin da za su ziyarci bankunan kasuwancin su daban-daban a cikin wa’adin kwanaki 90 da aka ba su don musanya tsoffin takardun su na Naira da sabon kudin.

Emefiele ya ci gaba da cewa bai fahimci dalilin da ya sa za’a tsawaita wa’adin ba, kuma babban bankin ya yi duk mai yiwuwa wajen bai wa jama’a damar ajiye tsohon kudaden su kafin wa’adin.

Ya ce, domin ‘yan Najeriya su cika wa’adin, CBN ya gana da bankunan kasuwanci inda suka bukaci a tsawaita lokacin su na kasuwanci da kuma kwanakin aiki zuwa ranar Asabar.

Babban bankin na CBN ya sanya ranar Talata 31 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a gudanar da aikin rarraba tsofaffin takardun kudi yayin da ya bayyana a watan Oktoba na shekarar 2022 cewa zai sake fasalin kudin N200, N500, da N1,000.

Domin a kara yaduwa, tun daga lokacin ne CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci da su daina karbar kudaden sabbin takardun kudi a kan kantunan, maimakon haka su ajiye musu na’urorin su na Automated Teller Machines (ATM).

Sakamakon tafiyar hawainiya da sabbin takardun kudi na Naira, Majalisar Dattawa da ‘yan Najeriya da dama ke neman a jinkirta wa’adin.

Advertisement