Al'umma

Aure: Ango na neman a biya shi dala $20,000 bayan amarya ta wanke kwalliyar ta

Idan kana da rai babu abinda ba zaka gani ko ji ba. A yau wani babban labari ne na wani sabon ango a kasar Algeria dake a yankin Afrika ya maka mahaifin amaryar shi a gaban kotu shari’a inda ya bukaci kotun da ta umarci su da su biya shi tsabar kudi har dalar Amurka dubu ashiri ($20,000) sakamakon yauradar shi da aka yi.

Advertisement

Angon ya bayyanawa kotun cewa ya farka daga barci inda ya ya razana matuka ganin bakuwar fuska tare da shi a cikin gida inda ya zaci barauniya ce ta shigo mai gida.

Daga bisani angon cikin firgici ya gane cewa ashe amaryar da ya auro ce inda ya bayyana cewa hakan ba zata sabu ba domin sam ba abinda ya aura ne ya gani a gaban shi, inda nan ba tare da bata lokaci ba ya maka mahaifin amaryar a kotu kan zargin cuta cikin aminci inda ya bukaci a biya shi diyya ya fasa auren.

Advertisement

Advertisement