Laifuku

Atiku yayi Allah-wadai da kisan ɗalibar da ta yi ɓatanci ga Annabi [S.A.W] a Sokoto

Nayi Allah wadai da waɗanda da suka kashe wacce ta zagi Annabi (S.A.W) a Sokoto, kuma dole a hukunta su – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana hakanne akan shafin sa na Facebook cikin wannan daren, kamar yadda zaku gani a cikin wannan hoton dake ƙasa.

Mintuna kaɗan da yin fostin ɗin, musulmai suka yi ta ruwan zagi da cin mutunci akan tsohon mataimakin shugaban, inda bada dadewa ba, ya bada umurnin a goge fostin ɗin daga shafin nasa.

Back to top button