Al'umma

Atiku ya goge sakonnin da ya wallafa a Facebook, Twitter na Allah-wadai da kisan ɗaliba Deborah Samuel

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya goge wani sako da ya wallafa a shafin shi na Facebook da Twitter inda ya yi Allah-wadai da kisan Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke jihar Sokoto, mai mataki 200, da aka kashe kuma aka kona ranar Alhamis saboda zagin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Arewa Times Hausa ta ruwaito cewa dalibai maza sun yiwa dalibar dukan tsiya har ta kai ga kona ta a ranar Alhamis din da ta gabata sakamakon da zagin Annabi Muhammad ta hanyar dandalin WhatsApp.

Hukumar makarantar ta rufe harkokin ilimi har zuwa wani lokaci yayin da tashin hankali ya mamaye mazauna yankin.

Da yake mayar da martani kan lamarin a ranar Alhamis, Atiku a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya bayyana cewa dole ne a gurfanar da duk wadanda ke da hannu a kisan.

Ya rubuta, “Ba za a iya samun hujjar irin wannan mugun kisa ba. An kashe Deborah Samuel, kuma duk wadanda suka kashe ta dole ne a hukunta su. Ta’aziyyata ga yan uwa da abokan arziki.”

Sai dai wasu masu kishin addini da ke da sunan Musulunci sun mamaye sassan sharhin musamman a shafin Facebook, inda suka yi barazanar janye goyon bayan su ga aniyar Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Arewa Times Hausa ta gano a safiyar ranar Juma’a cewa bayan barazanar da ‘yan Arewa suka yi ta yi, an goge sakonnin daga kafar sadarwar Atiku.

Back to top button