Tsaro

Asari Dokubo ya bayyana dalilin da yasa gwamnatin Buhari ba za ta saki Nnamdi Kanu ba

Tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ya bayyana dalilin da yasa gwamnatin Buhari ta ki sakin shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

A lokacin da yake jawabi, Asari Dokubo ya bayyana cewa bai kamata a sako Nnamdi Kanu ba saboda ya haddasa tashin hankali, kuma tasirinsa ya sanya mabiyansa su yi barna a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.

A cewar rahoton Daily Times Nigeria, tsohon tsagerun Neja-Delta ne ya bayyana hakan a shafin Facebook a jiya.

Advertisement

Da yake karin haske, Asari Dokubo ya bayyana cewa mabiyansa (Kanu) za su dauki mkpuru ruwa (crystal methamphetamine), sannan su ci naman mutane, amma duk da haka suna son a gafarta wa Nnamdi Kanu a sake su.

Ya kuma kara da cewa, mabiya Kanu sukan yi garkuwa da sarakunan gargajiya, suna sanya bindiga a cikin bakunansu, saboda kawai su mutane ne da ba sa barin Biyafara ta zo.

Asari Dokubo ya tabbatar da cewa shi ne babban mai sukar shugaban kungiyar IPOB. Da yadda abubuwa ke tafiya a halin yanzu, da alama ba zai tsaya nan ba da jimawa ba.

Advertisement