Tsaro

Asari Dokubo na daukar matasa ƴan ƙabilar Ijaw, ƴan kungiyar asiri don yaƙar Biyafara – Inji IPOB

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta zargi tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Mujahid Asari-Dokubo, da daukar batattun matasa ƴan kabilar Ijaw, ƴan ƙungiyar asiri da kuma wasu tsagerun Neja Delta domin yakar shirin tabbatar da Biafra.

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar ta IPOB, Emma Powerful ya fitar a yammacin ranar Litinin, kungiyar ƴan awaren Igbo ta ce Dokubo da wasu ƴan siyasa dake adawa da kungiyar suna hada baki da jami’an tsaron Fulani, da fadar shugaban kasa, da miyagun ƴan siyasa, ciki har da wasu gwamnonin yankin Kudu maso Gabas, don haifar da hargitsi da rikici a Biafra.”

Kungiyar ta IPOB ta kuma yi gargadin cewa matakin da Dokubo da ƴan ta’addar suka dauka “za a tarwatsa su daga gidansa dake Cotonou, Jamhuriyar Benin, inda ya ke boye.”

Advertisement

“Rundunar leken asiri ta IPOB ta bankado wani shiri kan yadda Asari ke zagayawa yankunan gabar tekun kasar Biafra yana daukar ƴan kungiyar asiri da ƴan boko domin shiga cikin miyagu jami’an tsaron Najeriya, da miyagun ƴan siyasa ciki har da wasu gwamnonin yankin Kudu maso Gabas domin kai wa mutane hari tare da dora laifin a kan IPOB da kuma ƴan kungiyar ma’aikatan ESN,” wani bangare na sanarwar da aka bayar ga jaridar Ripples Nigeria ya bayyana.

Ya kamata jama’a su sani game da wannan mugunyar makirci a yankunan gabar ruwan Biafra na wasu tsirarun makiya na maido da kasar Biafra.

“Bai kamata su dauke mu da wasa ba. Masu fafutukar kafa kasar Biafra da ke zaune a yankunan gabar teku da na baya duk wani bangare ne na babbar kasarmu.

“Dole ne su fahimci cewa Asari da ƴan cin amana irin sa suna kokarin haifar da rudani tsakanin Igbo Biafra da Izon (Ijaw) Biyafara amma muna jiran yaran sa da aka dauka.

Kada ya yi tunanin cewa mu matsorata ne. Bari ya kuskura ya ga abin da za mu iya yi.

“Asari Dokubo ya kulla kwantiraginsa da gwamnatin Najeriya da wasu ’yan siyasar Kudu-maso-Gabas wajen daukar matasan kabilar Ijaw don yakar masu fafutukar kafa kasar Biafra irin da IPOB da ESN.

Advertisement