Siyasa

APC Za Ta Bace Daga Najeriya Bayan Zaben 2023 – Ayu

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi hasashen cewa a ranar Alhamis jam’iyyar APC za ta shiga duhu bayan zaben da za a yi a wata mai zuwa.

Ayu, wanda ya bayyana haka a jawabin shi a yayin taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP da aka gudanar a tsohon dakin taro na Mapo da ke birnin Ibadan a jihar Oyo, ya yi alfahari da cewa kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa da ke karkashin shi ya mayar da jam’iyyar ga talakawan Najeriya.

Ya kara da cewa babu wani mutum ko kungiya da za ta iya rike babbar jam’iyyar adawa.

Advertisement

Taron ya samu halartar dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo; tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, da dai sauran su.

Sai dai kuma gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde bai halarci taron ba a fili.

Makinde da wasu gwamnoni hudu – Nyesom Wike (Rivers), Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), da Okezie Ikpeazu (Abia) – suna neman shugaban jam’iyyar ya yi murabus a matsayin share fage na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar. Atiku Abubakar, a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Advertisement