Siyasa

An zaɓi Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan Zamfara

Sanata Muhammad Hassan Nasiha mai wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya ya zama sabon mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Advertisement

Majalisar dokokin jihar ce ta tantance Sanata Nasiha, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Nadin Nasiha ya biyo bayan tsige tsohon mataimakin gwamna Mahdi Gusau ne a yau Laraba 23/2/2022.

Advertisement

An tsige Gusau ne bayan rahoton da kwamitin bincike na alkalai ya gabatar ya same shi da laifin zargin da ake masa.

A zaman da aka ci gaba da zama kakakin majalisar, Nasiru Mua’zu, ya karanta wasikar da gwamnan jihar Bello Matawalle ya rubuta na tsayar da Sanata Muhammad a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Advertisement