Labarai

An Yanke Wa Sojoji 25 Hukuncin Kisa Bisa Tserewa Makiya

An yanke wa sojoji 25 da ake zargi da tserewa yaki da ‘yan tawayen M23 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo hukuncin kisa.

Kotun soji ta Butembo da ke lardin Kivu ta Arewa ta yanke hukuncin ne a ranar Larabar da ta gabata, inda ta zarge su da laifin tserewa makiya, lalata alburusai na yaki da kuma karya umarni.

“Na same su da laifi kuma na yanke wa kowannen su hukuncin kisa,” in ji Kanar Kabeya Ya Hanu, shugaban kotun soji.

An dai kafa kotun ne kusa da inda aka gwabza fada tsakanin sojojin Kongo da mayakan M23 da nufin hana sojoji tserewa daga fagen daga.

Jules Muvweko daya daga cikin lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma sun bayyana a gaban kotun soji guda 31 da suka hada da sojoji 27 da matansu farar hula hudu.

An dai wanke matan hudu ne yayin da aka yanke wa soja daya hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samunsa da laifin yin fashi. Babu tabbas kan hukuncin da aka yanke wa sojan na karshe.

Tare da Al Jazeera