Wasanni

An Yanke Wa Dan Wasan Barca Hukuncin Zaman Gidan Yari, Babu Beli

An yanke wa tsohon dan wasan Barcelona, Dani Alves hukuncin zaman gidan yari bisa zargin shi da yi wa wata mata fyade.

An kama matashin mai shekaru 39 a safiyar Juma’a bayan wata mata mai shekaru 23 ta zarge shi da yin lalata da ita a wani gidan rawa na Barcelona a ranar 30 ga Disamba, 2022.

An dauki matakin ne bayan mai gabatar da kara na jihar da lauyan da ke kare macen, wanda ake zargin ya bukaci alkalin da ba a bayyana sunan shi ba da ya tura shi gidan yari yayin da ake ci gaba da bincike.

Advertisement

Dan wasan ya yarda cewa ya kasance a babban gidan rawa na birnin Sutton lokacin da ake zargin shi da aikata laifin jima’i. Jami’an ‘yan sanda da na kotun dai ba su yi wani karin haske ba kan hakikanin zargin ba.

Alves, wanda ya nuna rashin amincewar shi, ba a tuhume shi da wani laifi ba.

Advertisement