Tsaro

An San Maɓoya To Me Yasa Ba’a Kashe Ni Ba? Gwamnati Ce Ke Tunzura Ni Ina Kashe Mutane – Turji

Daya daga cikin ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a Najeriya, Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, ya tambayi gwamnati dalilin da yasa suka kyale shi a lokacin da suka kona gidan shi tare da kashe ‘yan uwan shi.

Turji fitaccen dan ta’adda ne wanda ya shahara wajen ta’addancin jihohin Zamfara, Sokoto da Niger. Shi da ‘yan kungiyarsa sun yi kisan gilla a Zamfara wanda yayi sanadin mutuwar sama da mutane 1,000, yara da mata. Akwai lokacin da a ranar 14 ga watan Nuwamba aka bayyana cewa ana neman shi da sauran ‘yan ta’adda, aka kuma za’a ba duk wanda yasa inda yake kyautar miliyan 5.

Da yake zantawa da daya daga cikin ‘yan jaridun Hausa Vanguard ta wayar tarho, ya bayyana bacin ran shi game da kisan da aka yiwa dan uwan shi da ‘yan uwan shi, sannan kuma ya bayyana yadda yake ji game da gidan shi da aka kona, yace ya amince da zaman lafiya yayi mulki a baya, amma gwamnati na son karya yarjejeniyar zaman lafiya da ta riga ta wanzu a tsakanin su da jama’a, yace ya amince da jami’an gwamnati akan su daina ta’adanci, amma sun zo gidan sun kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Advertisement

Turji yace yana mamakin ko da gaske ne gwamnati na son kashe shi ne saboda ya bar gidan mintuna biyu kafin a kona gidan sh. Yace, me yasa gwamnati ba ta kashe shi ba? Idan za su iya hango gidan shi su kashe duk wanda ke cikin shi, da har ni ya kamata su kashe, inji Turji.

Yace tun farko al’umma su san makiyin su domin gwamnati na tsokanar su ne domin su dauki fansa a kan talakawa saboda suna amfana da shi. Yace gwamnati na yaudarar jama’a da cewa suna son kawo karshen ‘yan fashi da makami, amma a zahiri su ne suka tsara hakan.

Turji ya kara da cewa zaman lafiya abu ne mai kima, kamar na gwamnati ta matsa masa ya zama mai yaki, a shirye yake ko dai yakin zaman lafiya ko kuma duk abin da gwamnati ke so. Yace yau watanni 5 ana zaman lafiya, amma ya ji an ci amanar yadda gwamnati ta tura mutane su kai hari gidan shi da na wasu mutanen da ke kusa da shi.

Sai dai ya bukaci gwamnati da ta biya shi kudi har miliyan ₦20 ko kuma ta fuskanci fushin shi.

Advertisement