Tsaro

An saki jagoran ƴan adawar Tanzaniya bayan watanni 7 a tsare

Wata kotu a Tanzaniya ta ba da umarnin a saki madugun yan adawa Freeman Mbowe bayan da masu gabatar da kara suka yi watsi da tuhumar da ake yi masa ta ta’addanci.

A wani hukunci da aka yanke ranar Juma’a, alkalin zaman Joachim Tiganga ya bada umarnin sakin Mbowe tare da wasu mutane uku da ake tuhuma bayan da masu gabatar da kara suka yi watsi da tuhumar da ake yi musu na bayar da kudaden don ta’addanci da hada baki.

“Yanzu an janye shari’ar daga kotu kuma ina ba da umarnin a saki wadanda ake zargin ba tare da wani sharadi ba,” inji Tiganga. “Ya kamata a sake su daga gidan yari.”

Advertisement

An kama Mbowe, shugaban jam’iyyar Chadema a watan Yuli tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar sa’o’i kadan kafin su gudanar da wani taron jama’a na neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima a Tanzaniya.

Advertisement