Laifuku

An Saki Aminu Muhammed Daga Gidan Yari Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar

Ɗalibin jami’ar tarayya dake Dutse a jihar Jigawa, Aminu Adamu Muhammed, da aka kama bisa wani sako da ya wallafa a shafin sh na Twitter a kan uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, daga karshe ya samu ‘yanci.

Arewa Times ta tattaro cewa an sako Muhammed a yammacin ranar Juma’a.

A baya Arewa Times ta ruwaito cewa Aisha Buhari ta janye karar da ta umurci ‘yan sanda zuwa cibiyar a kan yaron mai shekaru 23 da haihuwa.

Advertisement

Muhammed, dalibi a shekarar karshe a Sashen Kula da Muhalli da Dabbobi, a watan Yuni 2022 ta wallafa a shafin Twitter cewa Misis Buhari ta kara nauyi kwatsam bayan ta taka rawar gani wajen wawushe dukiyar kasa yayin da talakawa suka sha wahala a karkashin mulkin mijinta.

Advertisement