Al'umma

An saka wata mata sharar titi na kwanaki 30 S’saboda ta kiran makwabciyar ta karuwa

A kokarin da take na ganin ta dakatar da tuhume-tuhumen da ba daidai ba da ka iya haifar da karya doka da kuma tada fitina a tsakanin al’umma, kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a jihar Kano ta yankewa Mallama Rabi hukuncin hidima da al’umma sabodata kira makwabciyar ta karuwa.

Advertisement

Alkalin kotun shari’a, Halhalatul Khuza’i a hukuncin da ya yanke a ranar Laraba ya samu Mallama Rabi da laifin cin zarafi tare da kiran makwabciyar ta karuwa.

Mai shari’a Khuza’i a hukuncin da ya yanke ya umarci Mallama Rabi da ta share hanyar dake unguwar Rijiyar Zaki a Kano na tsawon kwanaki 30.

Advertisement

Da take magana bayan yanke hukuncin, Mallama Rabi ta shaidawa BBC News Hausa cewa ta gamsu cewa hukuncin bai wuce na share titi ba.

Irin wannan hukunci zai sa mutane su daina yin zargin da ba daidai ba a cikin al’umma. Babu shakka zai zama gargadi ga wasu cewa babu wanda ya fi karfin doka a cikin al’umma.

Advertisement