Taskar Labarai

An Rushe Hotel Din Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump

Tsohon shugaban Amurka na 45, Donald J. Trump ya samu kan jiya Alhamis cikin wani yanayi bayan an rushe wani Hotel mallakar shi da ake kira (Plaza hotel).

Amma dalilan da suka sa aka rushe ginin Hotel din na Trump shine; an bar Hotel kara-zube ba’a amfani da shi sannan kuma Hotel din bai samu wata kulawa ta musamman ba.

Tun a shekarar 2016 ne aka rufe Hotel din, sannan aka tsara cewa za’a rushe shi a watan feburerun wannan shekarar da muke ciki ta 2021, kamar yanda Arewa Times NG ta samu bayanan.

An kiyasta cewa Trump ya mallaki manya-manyan Hotel a Amurka har guda bakwai (7) kuma a wurare daban-daban.

Advertisement