Wasanni

An naɗa tsohon dan wasa Rigobert Song kocin Kamaru

Tsohon dan wasa Rigobert Song

An nada tsohon dan wasa Rigobert Song a matsayin kocin tawagar kwallon kafar Kamaru, wanda ya maye gurbin Toni Conceicao, bisa umarnin shugaban kasar, in ji ministan wasanni a ranar Litinin.

Advertisement

Conceicao na Portugal ya jagoranci Kamaru zuwa wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya kuma ya kai ta mataki na uku a gasar cin kofin Afrika da aka yi a gida a watan jiya.

Ministan wasanni Narcisse Mouelle Kombi ya ce shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya umarci hukumar kwallon kafar kasar da ta baiwa tsohon dan wasan baya na Liverpool Song aikin.

Advertisement

A wata sanarwa da Kombi ya fitar ta ce “A kan babban umarni daga shugaban kasar, an maye gurbin kocin kungiyar kwallon kafa ta maza, Mista Antonio Conceicao da Rigobert Song.”

“An gayyaci hukumar kwallon kafar Kamaru da ta dauki matakan da suka dace don aiwatar da wadannan manyan umarni cikin sauri da jituwa.”

Fecafoot ya tabbatar da “ƙarshen kwangilar” na Conceicao.

Kamaru za ta kara da Aljeriya mai rike da kofin nahiyar Afirka ta 2019 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a karshen wannan shekara a ranakun 25 da 29 ga Maris.

Advertisement