Kasuwanci

An kone gonar Obasanjo dake Benue kurmus bisa zargin batun rashin biyan diyya

An kona wata gonar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo dake karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar Benue a karshen makon da ya gabata.

Advertisement

An bayyana cewa gonakin Orchard, wanda ke yaduwa a fadin kasa mai fadin kadada 2,420 sun kunshi mangwaro da sauran yayan itatuwa.

Duk da cewa babu wanda ya iya sanin musabbabin tashin gobarar, ana zargin cewa watakila kauyukan ne da ba a biya su diyya na filin da suke amfani da su na gonar ba suka cinna wutar.

Advertisement

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban karamar hukumar Gwer, Emmanuel Otserga, ya ce gobarar ta tashi ne a sakamakon da gangan da masu yin barna suka yi, domin yadda ake kiyaye gonakin, babu yadda za a yi wuta ta tsallaka daga kowace kwata ta shiga gonar. .”

Otsega ya ce sama da rabin gonar gobarar ta cinye kafin jami’an kashe gobara su kashe ta.

“Mun samu rahoton cewa gonakin mangoro na Obasanjo da ke Howe na cin wuta, kuma na yi gaggawar sanar da duk masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya, kuma muka garzaya zuwa can ma hukumar kashe gobara ita ma ta zo amma har zuwa lokacin da za mu kashe gobarar. rabin gonar an riga an kona,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

A halin da ake ciki, Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Donald Ikyaaza, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mai yiwuwa wasu ‘yan asalin kasar ne suka kona gonar, inda suka yi ikirarin cewa ba a biya su diyya ba.

“Mutanena da suka je can sun ce mutanen na fafutukar neman diyya a fili. Watakila ba a biya wa filin diyya mai kyau ba, don haka ne suka yanke shawarar cinna wuta a gonar. Wannan shi ne kawai bayanin da na samu daga gare su,” ya kara da cewa.

Ikyaaza ya kuma koka da yadda mutanen da suka kashe gobarar suka yi musu fashi tare da lakada masa duka.

Ya ce, “Hakika mutanena a lokacin da suke dawowa da daddare, ‘yan fashi da makami sun kama su, suka yi musu mugun duka, suka kwashe duka wayoyinsu. Wannan ita ce diyyar da muka samu (ma’aikatan kashe gobara) na yakar gobarar da ta tashi a gonar Obasanjo. Ba duk gonar da aka kona ba. Wasu bishiyoyi suna nan; tsaba sun tsira.”

Advertisement