Nishaɗi

An Kone Gidan Mutumin Da Ya Umurci Fulani Makiyaya Da Su Bar Kudancin Najeriya

Wasu yan dabar da har yanzu ba’a kai ga gano ko su waye ba sun kone gidan Sunday Igbono, mutumin da a kwanan baya ya bawa fulani makiyaya a kudancin Najeriya, mussamman Jahar Oyo wa’adin kwana bakwai da su bar yankin.

Kwamishinan yan sanda na jahar Oyo ya tabbatar da aukuwa lamarin, inda yace wadansu yan bindiga da ba’a tantance ba cikin wadansu motoci gudu biyu kirar (Hummer Bus) da (Micra) suka kewaye gidan Ignono suna ta harbe-harbe ta ko ina kafin daga bisani su cinnawa gidan wuta da safiyar yau Talata.

Dakin zama, da wadansu gine-gine da kadarori sun kone dalilin aukuwa wannan lamarin. Inji hukumar yan sanda ta jahar ta Oyo.

Haka zalika, Sarkin fulanin jahar Oyo Alhaji Salihu Abdulkadir Ibarapa, wanda shima aka kone gidan sa a kwanan baya bisa zargin sa da satar mutane, ya musanta wannan zargin.

Back to top button