Tsaro

An kashe wani dalibi dan kasar Indiya a Ukraine lokacin da yake kokarin sayen abinci

An kashe wani dalibin likitancin Indiya a wani hari da aka kai a birnin Kharkiv na kasar Ukraine bayan da ya bar rumfar da yake mafaka domin sayen abinci.

Daya daga cikin abokan shi yace Naveen S Gyanagoudar, mai shekaru 22, yayi magana da shi jim kadan kafin rasuwar shi ranar Talata.

Dubban yan Indiya na cigaba da zama a Ukraine kuma suna neman a kwashe su bayan da sojojin Rasha suka mamaye ƙasar.

Indiya ta kaddamar da wani aiki don mayar da yan kasar ta gida amma tana fuskantar matsalolin kayan aiki.

Ma’aikatar harkokin wajen Indiya ta tabbatar da cewa Gyanagoudar ya mutu ne a wani hari da aka kai a Kharkiv, ta kuma ce tana tuntubar iyalan shi.

Advertisement