An Kashe Mutum (2) Bayan Yan Sanda Sun Bude Wuta Kan Masu Zanga-Zangar Kin Juyin Mulki A Kasar Myammar

, , Leave a comment

Rahotanni daga bangarori daban daban na duniya dake isowa, sun habarta da cewa an kashe mutum biyu bayan da yan sanda a kasar Myammar sun bude wuta akan masu zanga-zanga kin jinin juyin mulki.

Mutanen an kashe su ne a babban birni na biyu mafi girma a kasar, bayan hukumonin tsaro sun harba alburusai masu rai akan dandazon masu zanga-zanga, kamar yanda likitoci da masu kawo agaji suka bayyana.

READ ALSO:  Jigawa: Wani Magidanci Ya Binne Diyar Shi Da Ran Ta A Dakin Shi

Kasar Myammar tana cikin rudani dai tun bayan da sojojin kasar suka karbe mulki daga hannun shugaban farar hula Aung San Suu Kyi ranar 1 ga watannan da muke ciki na febureru.

Hukumomi a kasar a yan kwanakin nan suna mayarwa masu zanga-zangar kin juyin mulkin da martani mai karfin gaske wanda ya hada amfani da barkonon tsohuwa, alburusan roba da sauran su.

READ ALSO:  Munyi mamakin maganar IGP akan harin da aka kaiwa Gwamna Ortom - Akase

A cikin wani bidiyo ake nada kai tsaya a Facebook a lokacin da zanga-zangar ke faruwa ana iya jin karar harbin bindigogi.