Labarai

An Kashe Mutane Uku Bayan Masu Zanga-Zanga Sun Yi Yunkurin Fashe Ma’ajiyar Kayan Abinci A Yobe


Jami’an tsaro sun harbe wasu masu zanga-zanga uku a lokacin da suke kokarin lalata wuraren ajiyar abinci na wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa a garin Potiskum na jihar Yobe.

Potiskum na daya daga cikin garuruwan jihar Yobe dake karkashin dokar hana fita ta sa’o’i 24.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a lokacin da matasan masu zanga-zangar suka bijirewa dokar hana fita tare da yin yunkurin lalata kayayyakin.

An ce wasu da dama sun jikkata kuma an kai su asibiti domin yi musu magani.

An gudanar da Sallar Jana’izar marigayan nan take bayan Sallar Juma’a a fadar Sarkin Pataskum.

A halin da ake ciki a Damaturu babban birnin jihar ya kasance cikin kwanciyar hankali da lumana domin babu wata kungiya da ta fito domin gudanar da zanga-zanga a rana ta biyu na zanga-zangar a fadin kasar.

Wakilin Daily Post ya ruwaito cewa mazauna yankin sun yi kaura zuwa wuraren sana’o’insu, yayin da suke yin taka-tsan-tsan saboda fargabar abin da ba a sani ba.

Har zuwa lokacin cika wannan rahoto, jami’an tsaro da suka hada da Sojoji, ‘yan sanda, NSCDC, DSS da ‘yan banga sun girke a wasu muhimman wurare a cikin babban birnin Damaturu.