Labarai

An Kashe Mutane 2 A Zanga-Zangar Adawa Da Rushe Masallatai 19 A Habasha

An kashe mutane biyu, wasu da dama sun jikkata, sama da 100 ne ke tsare a hannun ‘yan sanda a zanga-zangar adawa da musulmi suka yi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, Ethiopia.

Bayan Sallar Juma’a, Musulman Habasha sun hallara a babban masallacin Anwar, babban birnin Addis Ababa, domin nuna adawa da rusa masallatai sama da 19 a birnin Sheger.

A cewar wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Addis Ababa ta fitar a daren jiya, mutanen biyu da aka kashe sun mutu ne bayan an tura su asibiti domin yi musu magani. Sanarwar ba ta ambaci ko ‘yan sanda ne suka kashe su ba.

Wadanda aka kashen dai su ne Siraj Mohamed da Abubakar Elias, dukkansu mazauna birnin.

Advertisement