Tsaro

An kashe mutane 13 a harin da ISWAP ta kai a wasu kauyuka 4 a Borno

Akalla mutane 13 ne aka ruwaito cewa mayakan kungiyar IS ta ISWAP sun kashe a cikin sa’o’i 48 a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ISWAP a ranar Lahadi ta kai hari kauyen Sabongari mai tazarar kilomita kadan daga garin Damboa a karamar hukumar Damboa ta jihar.

“Maharan sun kashe mutane bakwai,” ‘yan banga na yankin sun shaidawa DAILY POST ranar Lahadi.

Advertisement

Hakan dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan an kai wani hari a kauyukan Mandaragirau da Ghuma da ke karamar hukumar Biu.

Har ila yau, kasa da sa’o’i 48 da ‘yan ta’addan suka kai hari kauyen Kautikari da ke garin Chibok, inda suka kashe mutane da dama.

Mazauna kauyen Mandaragirau sun ce wannan shi ne karo na biyu da maharan za su kai hari kauyen nasu cikin watan Fabrairu.

A cewarsu, a karon farko sun zo ne suka yi awon gaba da wasu samarin kauyen, wadanda har yanzu ake garkuwa da su.

Harin da aka kai a kauyen Mandaragirau ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkata da dama kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

“A kauyen Ghuma, sun yi garkuwa da ‘yan mata biyu tare da wawashe kayan abinci. Sun kuma lalata shaguna tare da kwashe wasu dabbobi da su.” Wani Umar Audu ya shaida wa wakilinmu.

Advertisement