Tsaro

An Kashe Mashahurin Ɗan Ta’adda, Kachalla Gudau Da Wasu Ƴan Bindiga

Kwanaki hudu bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya aniyar gwamnatin shi na karfafa nasarorin da aka samu a fannin tsaro, sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga da dama ciki har da Ibrahim Kachalla Gudau.

Gudau, wanda ya shahara kuma daya daga cikin manyan ‘yan fashi da makami, ya jagoranci wata kungiyar da ke yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a Kafuna, Katsina, Zamfara da kuma wani bangare na Jamhuriyar Nijar.

An yi imanin cewa ’yan kungiyar Gudau sun kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da Civil Defence guda bakwai wadanda ‘yan bindiga suka yi wa kwanton bauna a jihar Kaduna a lokacin da suke bakin aiki a makon jiya.

Advertisement

Kamar yadda bayanan sirri suka nuna, Gudau, wanda gawar shi ta yadu a shafukan sada zumunta na yanar gizo, na daya daga cikin wadanda sojojin suka kashe yayin da suka dakile wani hari a kauyen Kankami da ke jihar Kaduna.

Advertisement