Ƙetare

An Karkatar Da Akalar Jirgin Da Ya Tashi Zuwa Ingila Bayan Samun Rahotan ‘Bam’ A Cikin Jirgin

Jirgin EasyJet daga Krakaw na kasar Poland zuwa birnin Bristol na kasar Birtaniya an karkatar da shi zuwa Jamhuriyar Czech bayan da aka gano wani ‘bam mai yuwuwa’ a cikin shi.

Filin tashi da saukar jiragen sama na Prague ya sanar da cewa an tilastawa kamfanin jirgin EasyJet mai rahusa karkatar da hanyar shi bayan da aka samu rahoton wani abin fashewa da ake kyautata zaton bam ne na cikin gida.

An karkatar da Jirgin na EasyJet mai lamba 6276 da karfe 10:50 na daren Lahadi, kuma ya sauka lafiya a babban birnin Jamhuriyar Czech bayan sa’a daya a cikin jirgin na sa’o’i biyu da rabi, kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

Advertisement

Filin jirgin saman Prague ya wallafa a shafin shi na Twitter cewa: ‘An ba da rahoton yiwuwar bam a cikin jirgin.

“Jirgin EasyJet mai lamba EZY6276 daga Krakow zuwa Bristol an karkatar da shi zuwa Prague a daren jiya bayan da aka samu ‘bam mai yuwuwa’ a cikin jirgin.

“Dukkan ayyuka don tabbatar da amincin fasinjoji da duk zirga-zirgar jiragen sama ‘yan sandan Jamhuriyar Czech ne suka aiwatar.”

‘Yan sandan Czech sun ce an aike da ‘masu fasaha na pyrotechnics’ zuwa wurin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike da kuma zubar da na’urar da ake tuhuma.

Ana kyautata zaton an dauke fasinjoji ne daga cikin jirgin yayin da jami’an ‘yan sanda ke gudanar da bincike.

Jami’an filin jirgin saman Prague daga baya sun kara da cewa “ba a sami wani abu mai hatsari a cikin jirgin ba bayan binciken pyrotechnic.”

Shafin yanar gizo na EasyJet ya nuna an shirya wani jirgin da zai biyo baya domin wasu fasinjoji da suka tashi daga Prague jim kadan bayan karfe 11 na dare agogon kasar da ke kan hanyar zuwa Bristol.

Advertisement