Tsaro

An kama yan Najeriya 12 bisa zargin zambar Intanet a Ghana

Rundunar yan sanda ta Bole a yankin Savannah a kasar Ghana ta kama wasu yan Najeriya 12 bisa zargin su da hannu a aikata laifuka ta Intanet.

Kamen na farko ya shafi mutane tara ne, wadanda aka kama a kusa da garin Bole. Suna da wasu na’urorin lantarki a hannunsu.

Sun hada da Kelechi Chukwudoluwe mai shekaru 30 da Ibeneme Precious mai shekaru 20 da Nelson Chinedu da Emmanuel Ifanyi Chukwu mai shekaru 23. Sauran sun hada da Chukwu Eneke George mai shekaru 19 da Chibuzor Nweke da Mmaduabuchi Miracle mai shekaru 20 da Peter Eboh mai shekaru 23 da Kwukwe Makachi mai shekaru 30.

Advertisement

A cewar rundunar ‘yan sandan Bole, binciken da aka gudanar a dakunansu ya kai ga kwato kwamfutoci 11 da wayoyin hannu 13.

A Sawaba da ke unguwar Bole, jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutane uku da ake zargin Joshua Wuneh mai shekaru 24 da Ugwu John mai shekaru 21 da Samuel Chibueze mai shekaru 25.

An gano wasu kwamfutoci da wayoyin hannu a hannunsu. Rundunar ta kuma gano CFA 2000, N1500, katin SIM na Airtel guda biyu, modem daya, belun kunne guda biyu, da kuma wata jaka mai dauke da GH¢25.

Wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda suna taimakawa da bincike.

Advertisement