Al'umma

An kama wasu mutane 3 da ake zargin suna sayar da kasusuwan mutane a Taraba

Wadanda ake zargi dauke da kasusuwan mutane a hannun su

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, sun kama wasu mutane uku da ake zargin masu girbin sassan jikin dan adam ne a jihar Taraba.

Advertisement

A cewar SaharaReporters, an kama wadanda ake zargin ne bayan an gano busassun kasusuwan mutane guda uku tare da su a garin Gembu, hedikwatar karamar hukumar Sardauna ta jihar.

Kakakin hukumar, Godwin Peter, wanda ya tabbatar da kamun ya ce, “Eh, mutane uku ne mutanen karamar hukumar Sardauna da ke jihar suka kama, an kama su da kashin mutane, suna sayar da kasusuwan mutane.

Advertisement

“An kama su ne a ranar Talata, 1 ga Maris, 2022.”

Masu sayar kasusuwan mutane

Advertisement