Tsaro

An kama Sojoji 2 na kasar Rasha lokacin da suke neman man fetur a Ukraine

Yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine yayi kamari, an kama sojojin Rasha dama tare da kashe su a Ukraine. Shugaban kasar Ukraine ya samu labarin cewa sama da sojojin Rasha 100,000 ne suka mamaye yankin su.

Sakamakon mamayewar, fararen hula a Ukraine sun fara shiga soja don yakar su da kuma kare kasar su. Hatta tsohon shugaban kasar Ukraine ya shiga yakin.

Sai dai abin takaicin shine, an bayar da rahoton cewa jami’an yan sandan Ukraine sun kama wasu sojojin Rasha biyu a Shevchenkove na yankin Kharkiv, a lokacin da suka je ofishin yan sandan Ukraine da ke yankin domin neman man fetur a yayin da man motar su ua kare.

Advertisement

A cewar sakon da wakilin tsaro a Kyiv Independent ya yaɗa, an kwato katin shaida na sojojin Rasha daga hannun su bayan kama su.

Advertisement