Al'umma

An kama iyayen da suka yiwa malamin makaranta duka tare da ƴan daba a Ogun

Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani Oyedele Nutai Joseph da matarsa, Elizabeth Joseph bisa laifin kai farmaki makarantar dansu, Toyon High School da ke unguwar Ado-Odo Ota a jihar tare da wasu yan daba domin kai wa wani malami, Abel Thomas hari bisa zarginsa da dukan dansu dalibin SS3 na makarantar.

Kakakin rundunar yan sandan, DSP Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai da jaridar Blueprint ranar Laraba, a Abeokuta.

Oyeyemi ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan kiran da yan sanda suka yi a hedikwatar su ta Ado odo daga makarantar cewa iyayen daya daga cikin dalibansu na cikin makarantar tare da yan baranda inda suka yiwa wani malaminsu duka tare da raunata shi.

Advertisement

Da aka yi wannan kiran, DPO Ado Odo, SP Arowojeun Michael, ya yi gaggawar jagorantar mutanensa zuwa makarantar inda aka damke ma’auratan yayin da sauran abokan aikin su suka tsere.

Binciken farko ya nuna cewa malamin, Abel Thomas, ya yiwa wani dalibi SS3 na makarantar, Joshua Joseph ya da ladantar da shi, inda ya je gida ya sanar da iyayensa cewa malamin ya yi masa duka.

“Da jin ta bakin dansu, iyayen da suka ji cewa malamin ba shi da hurumin dukan dansu kan ko wane dalili, sai suka kira wasu yan baranda suka mamaye makarantar.

Advertisement