Tsaro

An ji karar harbe-harbe a kusa da gidan gwamnati a babban birnin Ukraine

Rasha ta matsa kaimi wajen mamaye kasar Ukraine zuwa wajen babban birnin kasar a yau Juma’a bayan ta kai hare-hare ta sama kan garuruwa da sansanonin soji tare da aikewa da sojoji da tankokin yaki daga bangarori uku.

An yi ta tashin bama-bamai tun kafin wayewar gari a birnin Kyiv kuma daga bisani an ji karar harbe-harbe a kusa da sashin gwamnati a daidai lokacin da shugabannin kasashen yammacin duniya suka shirya wani taron gaggawa kuma shugaban Ukraine ya nemi taimakon kasa da kasa domin dakile harin da ka iya hambarar da gwamnatinsa ta dimokuradiyya, da kuma haddasa hasarar rayuka da dama da kuma barnar tattalin arzikin duniya.

Daga cikin alamun da ke nuna cewa ana kara fuskantar barazana a babban birnin Ukraine, sojojin kasar sun fada jiya Juma’a cewa, an ga wasu gungun ‘yan leken asirin Rasha da masu zagon kasa a wata gundumar Kyiv mai tazarar kilomita 5 arewa da tsakiyar birnin.

Advertisement

Tun da farko dai rundunar sojin kasar ta ce dakarun kasar Rasha sun kama wasu motocin sojin Ukraine guda biyu da wasu kafofi inda suka nufi birnin da nufin yin kutse da sunan ‘yan kasar.

Advertisement